<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>277</hymn_number>
<title>Ina Cikin Yaƙi, Magautana Kuwa LW277</title>
<lyrics>[V1]
 1) Ina cikin yaƙi, magautana kuwa
 Shaiɗan ne da duniya, duk da zuciyata.
 Ubangiji Yesu, ji addu'ata,
 Ban da taimakonka sai in halaka.

[V2]
 2) Ni ban isa kome cikin yaƙi ba.
 Sai da taimakonka zan ƙori Shaiɗan.
 In ka bar ni, Yesu, mutuwa zan yi.
 Yesu, na roƙe ka, riƙe ni yanzu.

[V3]
 3) Kowane Mai Binka, in ya kira ka,
 Za ka taimake shi cikin yaƙinsa.
 In ka ba ni iko, zan yi nasara.
 Na roƙe ka, Yesu, kai ni lafiya.</lyrics>
</song>